Yau ta ke Sallah a kasashen musulmi | Labarai | DW | 31.07.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yau ta ke Sallah a kasashen musulmi

Musulmi a fadin duniya na shagulgulan babbar sallah. A ranar Alhamis mahajjata suka yi hawan Arfa da ke zama kololuwa na aikin hajji inda a nan ne Manzon Allah S.A.W ya gabatar da hudubarsa ta karshe.

A kasar Indonesia wadda ke da mafi yawan musulmi a duniya, jama'a sanye da kyallen rufe baki da hanci sun gudanar da sallar idi a cikin masallatai tare da takaita zirga zirgar jama'a a kan tituna.

Jami'an kiwon lafiya sun baiyana fargabar yaduwar cutar corona yayin tarukan ibada musamman a masallatai da gidaje ko kuma wajen tafiye tafiye domin ziyara.

A waje guda Sarki Salman bin Abdul'aziz na Saudiyya a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter jim kadan bayan fitowarsa daga asibiti ya taya al'ummar musulmi murnar sallar layya.

Shi ma a nasa bangaren Firaministan Australia Scott Morrison ya bukaci musulmi a kasarsa su gudanar da bukukuwan sallah a cikin gidajensu