1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yarjejeniyar zaman lafiya ga zaɓen ƙasar Ghana

November 29, 2012

A ranar bakwai ga watan Disamba al'umar Ghana za su gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na 'yan majalisar dokoki. Ƙasar dai na zaman abar koyi wajen shirya zaɓe mai tsafta a tsakanin ƙasaashen Afirka.

https://p.dw.com/p/16snC
Hoto: Reuters

Shuagabannin jam'iyyun siyasar ƙasar Ghana, da za su tsayawa takarar neman shugabancin ƙasar a zaɓen da za a gudanar nan da mako ɗaya sun rataba hannu a kan wata yarjejeniya na gudanar da harkokin su na siyasa ba tare da wasu tashe tashen hankula ba, yarjejeniyar dai an sanya mata suna "Ƙudurin Kumasi", wato bnirnin da aka yi taron cimma yarjejeniyar.

Wannan taron ƙulla yarjejeniya a tsakanin 'yan takarar da aka gudanar a birnin na Kumasi dake jihar Ashanti ya samu halartar dukkannen shuagabannin jam'iyyun siyasar ƙasar ta Ghana sai kuma tsoffin shugabannin ƙasa Jerry John Rawlings da kuma John Agyekum Kuffour a matsayin shaidu da kuma iyayen ƙasa.

Ga dai abinda yarjejeniyar ta kunsa a bakin babbar lauyar gwamnati Georgina Theodora Wood.

"Yarjejeniyar da aka ƙulla a birnin Kumasi, ɗaukar matsaya ɗaya ta ganin cewa an gudanar da zaɓe cikin lumana, kiyaye tashe tashen hankula a lokacin zaɓe da kuma guje wa rashin adalci."

Ghana ta zama ja gaba a kyakkyawan mulki

Ko da yake ƙasar ta Ghana ta na samun jinjinawa a duniya baki ɗaya dangane da ci-gaban da ta samu a fannin demokraɗiyya, amma akwai wasu ungwanni a cikin ƙasar kamar Odododiodio inda ake samun tashe tashen hankula masu nasaba da siyasa, inda ma a cikin watan Agusta aka gwabza faɗa mai tsanani inda mutane da dama suka samu raunuka.

Evangelischer Kirchentag in Dresden - John A. Kufuor
John A. Kufuor tsohon shzgaban GhanaHoto: picture-alliance/dpa

Benjamin Quaye mazaunin unguwar Odododiodio ne ga abin da yake cewa game da wannan yarjejeniya da aka ƙulla.

"Za a gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali na yi imanin hakan, ba za a samu tashe tashen hankula ba, yanzu Ghana mu ma muna son mu yi koyi da ƙasar Amirka wadda ta yi zaɓe cikin tsafta, kuma bayan bayyana sakamakon al'ummar ƙasa ta sake haɗewa ba tare da la'akari da jam'iya ba, don haka Ghana za ta yi zaɓe cikin kwanciyar hankali."

Yanzu haka sauran kwanaki ƙalilan a gudanar da zaɓe a ƙasar ta Ghana. Jami'an tsaro kuma sun bayyana unguwanni fiye da dubu ɗaya da ba za a rasa 'yan matsaloli ba, ana nan kuma ana shaci faɗi game da wasu jawabai da ɗan takarar jam'iyyar NPP Nana Akuffo Addo ya taɓa yi a wasu kwanaki can baya inda ya ce ko da ana ha maza ha mata, magoya bayansa za su yi hoɓasa domin su sake ƙwato iko daga jam'iyyar NDC. Romeo Adoglah wani mai sharhi ne a kan siyasa ga abinda yake cewa.

Ghana John Atta Mills und Jerry Rawlings
Jerry Rawlings da marigayi John Atta MillsHoto: Getty Images

"A ra'ayi na za a gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali, amma kuma waɗannan ungwannin fiye da dubu ɗaya da jami'an tsaro suka gano kamata yayi su ɗau matakai masu ƙwari na magance su, domin ko yaya aka yi wasu sun tayar da jijiyar wuya."

Ko da yake kasar Ghana ta yi fice a fannin mulkin demokraɗiyya, kuma ƙasa ce mai tarihin miƙa mulki cikin ruwan sanyi ba tare da wani ka ce na ce ko tashe-tashen hankula ba. Tambayar dai ake ita ce ko a wannan karon ma za ta ba wa mara ɗa kunya?

Mawallafa: Isaac Kalöedzi / Mariam Mohammed Sissy
Edita: Mohammad Nasiru Awal