Yarjejeniyar zaman lafiya a Mali
March 1, 2015Talla
Gwamnatin kasar ta Mali ta sa hannun zaman lafiya tsakaninta da wasu kungiyoyin mayakan arewacin kasar, to amma babbar kungiyar Abzinawa ta bukaci a bata lokaci, domin ta samu tuntubar magoya bayanta, talakawan yankin da suka kira Azawad. An dai wata takwas ana tattaunawar zaman lafiya, tsakanin gwamnatin Mali da 'yan tawayen arewacin kasar, wadanda suka nemi ballewa don kafa kasar kansu mai suna Azawad.