Yarjejeniyar zaman lafiya a Kongo | Zamantakewa | DW | 22.01.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Yarjejeniyar zaman lafiya a Kongo

A Janhuriyar Democraɗiyyar Kongo,an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin gwamnati da wakilan 'yan tawaye a garin Goma dake zama cibiyar gunduwar Kivu a gabashin wannan ƙasar

default

Yarara Kanana a garin Goma,Kongo.

An kiyasta cewar kimanin mutane million 5 da dubu ɗari huɗu ne suka rasa rayukan su a Kongo daga shekara ta 1998.Hukumar agajin kasa da kasa ta bayyana rikicin na kongo na mai zama mafi girman irin sa da aka rasa rayuka fiye da kowane rikici,tun bayan yakin duniya na biyu.

Shima komitin agajin kasa da kasa dake cibiya a birnin New York din Amurka,cewa yayi mutane dubu 45 ne ke rasa rayukansu a kowane wata awannan kasa dake yankin tsakiyar Afirka,shekaru biyar bayan kawo karshen yakin ƙasar a shekara ta 2003.

Zebede Agasore dake shugabantar 'yan kabilar tutsin Kongon yace sun amince da yarjejeniyar.."mun rattaba hannu akan yarjejeniyar ,bayan tattaunawa da ɗaya daga cikin komitocin dake shirya wannan taro.Mun cimma batutuwa da dama .bisa dukkan alamu kowa na muradin zaman lafiya ,dangane da haka ne muka amince da cimma wannan yarjejeniya."

Ana kwatanta asaran rayuka da Kongo tayi da kasancewa daidai da yawan alummomin ƙasar Denmark na yanzu.Shugaban hukumar agajin kasa da kasa George Rupp,yace duk da kawo karshe yaki a shekara ta 2003,har yanzu mutanen wannan kasa na fama da matsanancin talauci kawo yanzu.

Wasu daga cikin su kuwa na rasa rayukan su ne sakamakon kamuwa da cututtuka da zaa iya maganta ko kuma kare kamuwa dasu,kamar Malaria ,cutar amai da gudawa ,Sankarau da karancin abinci mai gina jiki,musamman a bangare kananan yara.

Adangane da batun 'yan gudun hijira da suka tsere daga matsugunnen su kuwa shugaban Tutsi Agasore yace sun amince da komowan dukkannin su gida.Zaa tsara yadda za a komo dasu tsakanin gwamnatocin Kongo da Burundi da hukumar kula da 'yangudun hijira Majalisar Ɗunkin Duniya da Rwanda da Tanzania kana da Uganda.

Ɓangarorin 'yan adawa da gwamnatin Kongon,sun cimma wannan yxarjejeniya ne a garin Goma dake gabashin ƙasar,inda nan ne kuma 'yan tawayen sukayi ta arangama da dakarun gwamnati na lokaci mai tsawo.

Shima kakakin tattaunawar sulhun da aka gudanar a Goma,Vital Kamere cewa yayi bayan yaki ya barke,babu wanda yasan lokacin da zai zo karshe.Sai babbar farin cikin su ayau shine an cimmam warware wannan matsala da ta dauki tsawon lokaci tana yiwa kasar lahani.

Binciken da wannan kungiya ta gudanar tsakanin Janairun shekarata 2006 zuwa watan Aprilun 2007 dai,ya nunar dacewa sama da mutane dubu 700 ne suka rasa rayukan su tsawon wannan lokaci,mafi yawansu kuwa yara wadanda shekarun su basu shige biyar da haihuwa ba.

Rikicin Kongon dai ya samo asali ne da shekarun mulkin danniya na tsohon shugaba Mobutu Sese Seko,wanda 'yan adawa suka kifar da gwamnatin sa a 1997,wanda ya jefa kasar cikin tashin hankali na yake-yake,rikicin daya samu tallafi daga wasu kungiyoyin sojin sakai na ketare guda shida.

A shekara ta 2006 nedai aka gudanar da zaɓen farko cikin tarihin ƙasar,wanda ya ɗora shugaba Joseph Kabila akan karagar shugabanci.Sai dai zargin da akewa gwamnatin sa da cin hanci da rashawa ,ya haifar da tafiyar hawainiya wajen shawo kian matsaloli na rayuwa da alummomin Kongon ke fama dasu.

Cimma wannan yarjejeniya tsakanin ɓangarorin adawan da gwamnatin Janhuriyar Democraɗiyyar Kongon dai,batu ne idan ya ɗore zai zame babban tarihi a rikici mafi muni da akafi asaran rayuka a Afrika.