Yarjejeniyar tsagaita wuta a Mali | Labarai | DW | 05.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yarjejeniyar tsagaita wuta a Mali

Gwamnatin kasar Mali da 'yan tawayen Abzinawan kasar sun sanya hannu kan wata yarjejeniya da ta amince da tsagaita a tsakaninsu.

'Yan twayen Abzinawa na Mali da ke rikici da gwamnati

'Yan twayen Abzinawa na Mali da ke rikici da gwamnati

Hakan dai ya bada karfin gwiwa wajen cimma yarjejeniyar sulhu da Majalisar Dinkin Duniya ta jima ta na kokarin ganin an cimma a tsakaninsu domin kawo karshen yakin da suka kwashe tsahon shekaru suna fafatawa da juna a arewacin kasar. Babban jakadan Majalisar Dinkin Duniya a Malin Mongi Hamdi ne ya sanar da hakan inda ya ce daya daga cikin matakan yarjejeniyar ya bukaci da a tsagaita wuta a garin Menaka da ke arewaci da kuma janyewar mayakan sa kai da ke goyon bayan gwamnatin ta Mali a yankin, inda ya ce za a maye gurbinsu da dakarun Majalisar Dinkin Duniya zuwa wani lokaci. Su dai 'yan tawayen Malin na fafutukar samar da 'yancin kan yankin Abzinawa ne wanda suka yiwa lakabi da Azawad.