Yarjejeniyar sulhun Mali na tangal-tangal | Labarai | DW | 24.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yarjejeniyar sulhun Mali na tangal-tangal

'Yan aware a yankin arewacin Mali wadanda aka fi sani da AZAWAD sun yi barazanar janyewa daga tattaunawar sulhu.

'Yan aware a yankin arewacin Mali wadanda aka fi sani da AZAWAD sun fitar da wata sanarwa, inda suka yi barazanar cewa za su dakatar da wakilansu daga aiki a kwamitin da aka girka, dan tafiyar da aiyukan samar da sulhu, har sai sadda suka rage samun matsala tsakaninsu da 'yan tawayen da ke samun goyon bayan gwamnati.

Wata arangamar da ta kunno kai, bayan da 'yan tawayen da ke goyon bayan gwamnati suka anshe garin Anefis daga hannun Azawad din ne ya janyo matsalar, ta wannan karon, abin da suka ce ya sabawa yarjejeniyar da Majalisar Dinkin Duniya ta jagoranta tsakanin bangarorin biyu a watan Yunin da ya gabata.

Tuni dai wadanda suka shiga tsakanin wannan yarjejeniya na watan Yuni suka bukaci bangarorin biyu da su mutunta tanadin wannan yarjejeniya, su sako fursunonin yakin da suke tsare da su domin cire duk wani abin da zai kawo rashin yadda a tafiyar da ake yi na samar da sulhu. Tare da tallafin dakarun wanzar da zaman lafiyar Majalisar Dinkin Duniya ta MINUSMA, Mali ke kokarin dakatar da tashe-tashen hankulan da ke afkuwa tsakaninta da Abzinawa.