Yarjejeniyar sulhu tsakanin yan tawaye da gwamnatin Mali
July 4, 2006Sanarwar daga Algers babban birnin Algeria, ta ce, an rattaba hannu a kan yarjejeniyar zaman lahia, tsakanin yan tawaye da gwamnatin ƙasar Mali.
A cimma wannan mataki, tare haɗin gwiwar gwamnatin Alegria, da ta shiga tsakani.
Idan ba a manta ba, a watan da ya gabata yan tawayen ƙasar Mali, sun kai hare hare, a yankin Kidal, inda su ka yi awan gaba, da makama da kuma dukiyoyi masu yawa.
Daga jerin buƙatocin su, yan tawaye sun nemi gwamnati ta kauttata makomar yankin su, sannan a ƙara masa cikkaken yanci.
Bayan kwanaki na shawarwari, sanarwar da aka bayana a yau, ta ce yan tawayen sun yi watsi da buƙatar yancin gashin kan Kidal.
Sannan a nata ɓangaren gwmanati, ta alƙawarta saka kuɗaɗe masu yawa, domin kauttata rayuwar al´ummomin kidal.
Bayan hare haren na watan da ya wuce, al´ummomin ƙasar Mali,, sun shiga zullumin sake ɓarkewar rikicin tawaye, irin wanda ya abku a shekarun1990.