Yarjejeniyar kasuwanci ta TTIP na shan suka | Labarai | DW | 17.09.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yarjejeniyar kasuwanci ta TTIP na shan suka

A sassa daban-daban na Jamus an yi zanga-zangar adawa da yarjejeniyar kasuwanci tsakanin Amirka da Turai ta TTIP, inda dubban 'yan adawa da shirin suka fita gangami.

Demonstration Ceta TTIP in Stuttgart

Masu zanga-zangar adawa da TTIP a Stuttgart

Dubban daruruwa na al'umma a Jamus sun hau kan titunan kasar a ranar Asabar din nan a wani gangami na nuna adawa da shirin kasuwancin bai daya tsakanin kasashen na Turai da Amirka karkashin yarjejeniyar kasuwanci mara shinge mai lakabin (TTIP). Abin da ke kara zama nakasu ga yarjejeniyar da yanzu ke cikin garari.

A cewar Roland Suess dan fafutika da ke adawa da tsarin duniya bai daya a kungiyar Attac da ke zama daya daga cikin kungiyoyi da suka tsara gangamin ya ce suna sa ran mutane 250,000 za su fito wannan zanga-zanga a fadin kasar ta Jamus ciki kuwa har da birnin Berlin da cibiyar hada-hadar kasuwancin kasar ta Jamus ta Frankfurt. Masu fafutika dai na cewa wannan yarjejeniya na da illoli ciki kuwa har da jawo rasa aikin yi a tsakanin al'umma da ke fama a yanzu.