Yaran da aka shiga da su Amirka na cikin rudani | Labarai | DW | 05.09.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yaran da aka shiga da su Amirka na cikin rudani

Gwamnatin Amirka ta kawo karshen shirin daina fitar da mutane wadanda aka shigar da su kasar suna yara lamarin da ya fusata 'yan fafutuka.

Gwamnatin Shugaba Donald Trump ta Amirka ta bayyana kawo karshen shirin tsame wadanda aka shigar kasar suna yara daga cikin wadanda za a kora zuwa kasashensu na asali. Gwamnatin ta ce shirin na tsohon Shugaba Barack Obama ya kawo karshe domin Amirkawa ba sa maraba da haka, kamar yadda minsitan sharia na kasar Jebb Sessions ya bayyana.

Tuni shugabannin siyasa da na 'yan kasuwa suka fara caccakar matakin na gwamnatin Amirka da zai shafi kimanin mutane 800,000 wadanda iyayensu suka shiga da su Amirka suna yara. Kuma lamarin zai iya illa ga tattalin arzikin Amirka saboda gabilin mutanen suna aiki da ke bunkasa tattalin arzikin kasar ta Amirka.