Yara matasa a lokacin yaƙin basasar Saliyo | Siyasa | DW | 13.11.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Yara matasa a lokacin yaƙin basasar Saliyo

A lokacin yaƙin basasar ƙasar kimanin mutane dubu 50 ne suka rasa rayukansu yayin da da dama suka tagayyara ciki har da yara da ake tilasawa aikin soji.

Da dama dai daga matasan garin Makeni da ke kudancin birnin Freetown a ƙasar ta Saliyo, sun samu mafuka a wata garejin koyon gyare gyaren motoci da wata ƙungiya mai zaman kanta ta kafa. Daya daga cikin matasa mai sunan Mahmoud Sessa yya share kusan shekaru 3 yana karbar horo a wannan gurin. Ko da yake a lokacin da yana aikin soji tare da 'yan tawaye, yana da wani lakanin suna wai shi Kiler,wato makashi,to saidai a yanzu bai amsa kira da sunan,ya ce a duk lokacin da aka kira shi da hakan sai ya ji ya fusata ransa ya bace. Mahmoud ya bayana nai dan takaitacen tarihinsa a lokacin da yana tare da 'yan tawayen ƙungiyar RUF bayan da suka aukawa kauyensu suka kuma tilasa masa kasancewa tare da su kai tsaye aka tilasa masa ya kashe 'yan uwansa.

"Bana son ni aikata abun.Da yake ina sa dan shakku,jaoran namu ya hasala ya aza mini yukuwa a wuya ya ce idan har ban aikata ba to ba shakka shi zai kashe ni bayan ya hallaka dangin nawa. nan da nan ni bi umurninsa ni harbe mutanen da ke gabana ciki har da yayana da yayan baban,ina harbi ina kuka,abun yana da tayarada hankali sosai ma."

A ranakun da Mahmoud ba ya aiki wato ranaikun futu,shi kan kai ziyara ga wasu abukaninsa wadanda suka yi aikin ina da kisan tare, wani sa'in ma suka raiara wakokin da aka koya musu a filin daga.

Yanzu haka a garin na Makeni mutane kalilan ne suka san tsohon tarihin Mahmud da shi da abukansa. Dauko mganar yakin basasa a kasar ta Saliyo abun ne da ke da matukar wahala domin ba kowa ne ke son tunin abunda ya faru a can bayan ba. A iya cewa a cikin kasar ba wanda lamarin bai shafa ba, ko ka rasa dan uwa ko aboki. Kamar Mahmoud da dama ne suka bar ainahin garuruwansu na asali bisa ga mumunan tarihin da ke lake a jikinsu. Bayan kammala yakin ne kungiyoyi daba daban suka dauki matakin horar da yaran da ayukan hannu bisa ga basu koyi duk wani aiki ba ban na kama bindiga da kuma yadda ake katse hannun dan adam wadanda su ma suka samu mafuka a wannan garin na Makeni kamar yadda Mhmoud ke cewa.

"Muna cikin sansanin wadanda aka yankewa sassan jikinsu a nan tsakiyar garin na Makeni. Gari ne musamman da aka ginawa mutanen da aka raba su da hannuwa ko kuma kafafuwa a lokacin yaki. Kawai 'yan masarorin dakuna ne ,da wasu 'yan itatuwa, can yara na wasa a gefe."

Wannan sansani na matsayi gari ne ga Adama Koroma wata mata da 'yan tawayen suka aukawa garin da ta ke tare da 'ya'yanta da mijinta suka share dare daya suna mata fyade bayan da suka karkashe kananan 'ya'yanta da mijinta kamin daga bisani ita ma su yanke mata hannuwa,a lokacin tana 'yar shekaru 18 da haifuwa.

"Za ka iya samun tsafin 'yan tawayen ko'ina a cikin Saliyo, to amman a gaskiya ban san wadanda suka mini wannan aikin ba saboda cikin dare ne abun ya faru. Koda na hadu da su a nan gurin ba zan iya tantance su ba. Na bar lamarin ga Allah da ya saka mini."

Duk da cewar kotun kasa da kasa da ke birnin Hage ta yankewa tsohon sugaban kasar Laberiya Charles Taillor hunkuncin daurin shekaru 50 a gidan kurku bisa laifin taimakawa mayakan 'yan tawayen,yanzu haka a kasar dubban mutane ne ke cikin cizon yatsa a dangane da irin ta'asin da aka aikata musu ko kuma ga iyalensu,yainda wasu kungiyoyi ke kira da a tona asirin wadanda aka san su da aikatawa wannan danya danyan aikin,wasu kwa kira suke yi da lokaci ya yi na a manta da komai a maida hankali ga gina kasar.

Mawallafi: DanielPelz/ Issoufou Mamane
Edita: Mohammad Nasiru Awal

Sauti da bidiyo akan labarin