′Yar adawa da ta bace a Ruwanda | Labarai | DW | 30.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yar adawa da ta bace a Ruwanda

Aristide Rwigara dan uwa ga wacce a ka kama ya fadawa kamfanin dillancin labaran Reuters cewa 'yan sanda ne suka dauketa tare da duk wanda ke a wajen lokacin da suka je gidanta.

Diane Shima Rwigara mai caccakar gwamnatin shugaba Paul Kagame da aka hana mata takara a zaben da ya gabata 'yan sanda ne suka dauketa tare da mambobi na iyalanta su hudu a cewar wani dan uwa gareta.

Aristide Rwigara ya fadawa kamfanin dillancin labaran Reuters cewa 'yan sanda ne suka dauketa tare da duk wanda ke a wajen lokacin da suka je gidanta akwai mahaifiyarsu da wasu kannensu a ciki. Aristide Rwigara da ke zaune a Amirka ya fadawa Reuters ta wayar tarho inda ya kafa hujja da wani da aka yi kamen a gaban idonsa.

'Yan sanda dai a wannan rana ta Laraba sun bayyana cewa sun yi bincike a gidanta bayan da suka sami wasu bayanai daga hukumar zaben kasar sai dai a bayanin da suka rubuta a shafin intanet sun ki amincewa da kamata da aka ce sun yi.

An dai shiga rudani daga bangaren na adawa bayan da aka nemi 'yar adawar Shima Rwigara sama ko kasa ba tare da an san inda take ba.