Yanukovych ya samu mafakar siyasa a Rasha | Labarai | DW | 28.02.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yanukovych ya samu mafakar siyasa a Rasha

Tsohon Shugaban Yukren ya yi shelar cewa shi ne shugaban ƙasa har yanzu. Hakazalika Viktor Yanukovych ya sanar da cewar zai yi jawabi a wannan Jumma'a.

A karon farko tsohon shugaban ƙasar Yukren Viktor Yanukovych wanda majalisar dokokin ƙasar ta tsige a makon jiya ya fito fili ya yi magana daga Rasha inda ya samu mafakar siyasa. Yanukovych ya yi watsi da sabuwar gwamnatin ta 'yan adawa wacce ta yi sanadiyar faduwar gwamnatinsa bayan da aka kwashe tsawon watannin suna yin bore.

Yanukovych ya kuma yi gargaɗin cewar har yanzu shi ne shugaban ƙasar na Yukren. Kuma nan gaba a yau jumma'a aka shirya tsohon shugaban zai yi wani taron manema labarai domin bayyana sabbin manufofinsa. Wasu rahotannin kuma da muka samu daga Yukren ɗin waɗanda ke yin karo da juna, na cewar kimanin wasu 'yan bindigar guda 50 sun karɓi iko da filin saukar jiragen sama na Simferopol da ke a cikin tsibirin Crimea, to sai dai hukumomn sun musunta labarin.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe