1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaHabasha

Yankin Tigray na fama da matsananciyar 'yunwa

Ahmed Salisu MAB
December 19, 2023

Yakin Tigray na kasar Habasha da ya yi fama da yaki a baya da mummunan fari na fuskantar karancin abinci, inda mutane da dama suka fice daga cikinsa yayin da wadanda ke zaune ke ci gaba da fuskantar kalubale babba.

https://p.dw.com/p/4aLYy
Yawancin wadanda ba su yi hijira don neman abinci ba na fama da 'yunwa a Tigray
Yawancin wadanda ba su yi hijira don neman abinci ba na fama da 'yunwa a TigrayHoto: Million Haileselassie Brhane/DW

Yankin na Tigray wanda yaki ya daidaita ya tsinci kansa a cikin yanayi na ja'ibar 'yunwa wadda da dama ke alakantawa da rashin wadatar ruwan sama wanda ya yi tasiri mummuna ga gonakin yankin da ma dabobin da jama'a ke kiwata. Wata mata da ke zaune a yankin mai suna Fitsum Woldegbriel ta ce irin barnar da farin dango suka yi da kuma karancin ruwan saman da aka samu a wasu sassan na Tigray ya haifar mummunan farin da ba a taba ganin irinsa.

Karin bayani: Habasha ta fada cikin wani sabon yaki

Fitsum Woldegbriel ta ce: " Duk abin da muka shuka bai fito ba saboda haka ba mu yi girbi ba. Ana fama da 'yunwa wanda ban taba ganin irinta ba. A baya idan aka samu irin wannan matsalar mutum zai iya zuwa wani wajen don ya roki abinci, amma yanzu ba mu da karfin yin hakan ba wanda ke iya zuwa ko ina ko ma yin hijira."

Halin da mutanen yankin suka shiga ya haifar da mace-mace na jama'a da kuma dabbobin da suke kiwatawa. Wannan ne ma ya sanya hukumomi a yankin mika kokon bararsu ga gwamnatin kasar ta Habasha da kuma kungiyoyin bada agaji kan su tallafa wa wanda wannan ibtila'i ya shafa don ceto rayuwarsu da kuma kawo karshen mace-macen da ake samu.

Jami'in gundumar Atsibi Mezgebe Girmay ya ce Tigray na bukatar agajin abinci
Jami'In gundumar Atsibi Mezgebe Girmay ya ce Tigray na bukatar agajin abinci Hoto: Million Haileselassie Brhane/DW

Mezgebe Girmay da ke zama jami'i na wata karamar hukuma da lamarin ya shafa ya ce: "Muna da kimanin mutane dubu 97 a wannan gunduma kuma kimanin mutum dubu 82 na cikin yanayi na tsananin bukatar abinci. Mun shiga wannan hali ne sanadiyyar karancin ruwan sha da aka samu. Yanzu haka ba abincin da jama'a da dabbobi za su ci, wanda hakan ya yi sanadin rasuwar mutane kimanin 111 da kuma dabbobin da yawansu ya kai 570. Ya kyautu gwamnati da kungiyoyin fararen hula su dauki matakin da ya dace don rage wahalar da mutane ke ciki."

Mahukunta a Addis Ababa sun ce sun fito da sabbin dabaru na ganin an tallafa wa wanda wannan ibtila'i ya shafa yayin da kungiyoyin bada agaj irin USAID suka ce cikin wannan watan za su ci gaba da rabon tallafin abinci ga mabukata a kasar Habasha baki daya.

Gebremariam Hagos na kokarin tsira da ragowar hatsi a gidansa da ke kauyen Atsibi.
Gebremariam Hagos na kokarin tsira da ragowar hatsi a gidansa da ke kauyen Atsibi.Hoto: Million Haileselassie Brhane/DW

Karin bayani:Al'umma na dakon kayan agaji a Ethiopiya 

Shi kuwa shirin abinci na Majalisar Dinkin Duniya wanda ya dakatar da rabon abincin da yake yi a kasar ta Habasha a watan Junin da ya gabata ya koma rabon da ya saba, kuma a yanzu ya ce kai tsaye yake aikin da mahukuntan gundumomin da ke fuskantar kalubale na karancin abinci da nufin ganin an sada abinci ga wanda ke bukatarsa.