1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yankin Goma na kudancin Kongo na cikin tashin hankali

November 20, 2012

Faɗa ya turnuƙe tsakanin ƙungiyar 'yan tawayen M23 da dakarun gwamnatin Kongo Kinshasa

https://p.dw.com/p/16m65
Hoto: Reuters

A ƙarshen makon da ya gabata ne mayaƙan ƙungiyar M 23 a jamhuriyar Demokraɗiyar Kongo suka aukawa yankunan Goma da ke kudancin ƙasar, inda rahotani suka ce aƙalla mutane 13 ne suka rasa rayuka. Rahotanin sun ci-gaba da cewar tare da haɗin gwiwar dakarun Ruanda ne 'yan tawayen suka samu nasararar kutsawa a yankin, inda suka kori sojojin gwamnati.
To saidai ya zuwa yanzu ƙura ta soma lafawa bayan da ,sojojin Majalisar Dinkin Duniya na Monusco suka yi yunƙurin ƙwato Goma. To saidai kakakin ƙungiyar 'yan tawayen ya ce ko kusa basu da buƙatar shiga birnin na Goma kuma yanzu haka yankin na riƙe a hannunsu.
Amma ya yi barazanar za su aukawa garin muddun dakarun gwamnatin suka yi ƙoƙarin ƙwato garin. Ana dai zargin gwamnatin Ruanda da kasancewa kanwa uwar gami a wannan rikicin Kongo bayan da Majalisar Dinkin Duniya ta bayanan wani rahotaon da ke zarginta da taimakawa dakarun M23, zargin da fadar mulkin Kigali ta yi watsi da shi.A safiyar wannan talata kuma rahotani dag Kongo sun 'yan tawayen M23 sun mamaye filin saukar jiragen sama na birnin Goma.

Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Yahouza Sadissou Madobi