1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yanke hukuncin kisa ga mutane hudu a Saudiya

September 22, 2014

Kotu a kasar Saudiya, ta yankewa wasu 'yan kasar guda hudu hukuncin kisa, bayan da aka samesu da laifin kasancewa cikin kungiyoyin 'yan ta'adda.

https://p.dw.com/p/1DGwY
Hoto: picture-alliance/AP Photo

A hannu daya kuma kotun da ke birnin Ryad, da kuma take duba harkokin da suka shafi ta'addanci, ta yanke wa wasu mutanen da suma ake zargin su da alaka da ta'addanci 20 hukuncin dauri na shekaru 23 a gidan kaso.

Ana zargin mutanen da laifin zuwa wasu kasashe domin yaki, a cikin wasu kungiyoyin ta'adda, sannan kuma da mallakar wasu sinadarai masu nauyin tonne biyar na hada bama-bamai. Sannan kuma an kamasu da laifi dana wasu bama-bamai ga wasu motoci da zimmar hallaka jami'an tsoron 'yan sanda a kasar ta Saudiya, amma kotun ta ce suna da kwanaki 30 na daukaka kara idan suna da ja kan wannan shari'a.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Suleiman Babayo