′Yan tawayen Siriya sun sako wasu yan Iran 48 | Labarai | DW | 09.01.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan tawayen Siriya sun sako wasu yan Iran 48

Yan tawayen sun sake su ne bayan da aka yi musanyar bursuna tsakanin su da gwamnatin Siriyar

Wani gidan telbijan na ƙasar Iran ya sanar da cewar gwamnatin Siriya ta fara sako wasu yan kaso na siyasa da ta ke tsare da su ,kusan mutun dubu biyu a cikin garuruwa daban daban na ƙasar .Waɗanda ta yi musayanrsu da wasu yan ƙasar Iran 48 da yan tawayen suke yin garkuwa da su.

Wani kakkakin wata Kungiyar ayyukan jin kai ta Islama IHH wada ke da cibiya a birnin Santanbul na Turkiya Serkan Nergis ya ce sun kwashe watannin da dama suna tattaunawa da gwamnatin da kuma yan tawayen domin cimma wannan shiri.Iraniyawan guda 48 yan tawayen sun yi awan gaba da su ne, tun a cikin watan Agustan da ya gabata.akan zargin da suke yi masu cewar suna tallafa ma gwamnatin Siriyar.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu