1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan tawayen M23 sun hada fada a Kwango

Mouhamadou Awal Balarabe
May 24, 2022

Wani sabon fada ya barke a kusa da birnin Goma da ke gabashin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango, kwana guda bayan da Ruwanda ta zargi kasar da kai farmaki kan wani kauye da ke kan iyakarta.

https://p.dw.com/p/4BoIG
Mai-Mai Milizen im Kongo
'Yan tawaye sun dade suna cin karensu babu babbaka a gabashin KwangoHoto: Dai Kurokawa/dpa/picture alliance

Mazauna yankin suka ce sun ji karar harbe-harbe a kewayen yankin Nyiragongo, inda aka  kai wa sojojin Kwango hari, lamarin da ya jikkata mutane biyu. Tun a jiya Litinin ne kasar Ruwanda ta ce wasu fararen hula sun jikkata sakamakon makamin roka da da aka harba daga Kwango zuwa wani yanki na iyakar kasarta da Kwango,  kuma ta yi kira da a gudanar da bincike cikin gaggawa kan lamarin.

Sai dai Majalisar Dinkin Duniya ta zargi kungiyar M23 da kai wannan hari. Dangantaka tsakanin Kwango da Ruwanda ta yi tsami tun bayan kisan kiyashin da aka yi a Ruwanda a shekarar 1994. musamman ma bayan da 'yan Hutu da ake zargi da neman murkushe 'yan Tutsi suka samu mafaka a Kwango.