Yan tawayen M23 ke iko da birnin Goma
November 21, 2012Bayan watanni da aka yi yan tawayen ƙungiyar M23 suna barazanar kame babban birnin lardin gabashin jamduriyar demokradiyyar Kwango wato birnin Goma, daga ƙarshen dai sun cimma burinsu. Birnin Goma mai mazauna kimanin miliyan daya, kana yake da dubban sojojin MDD, karɓe iko da yan tawaye suka yi da birnin wani babban koma bayane ga gwamnati shugaba Joseph Kabila. Sanin irin mahimmancin da birnin Goma ke da shi, ya sa gwamnatin ta faɗa cikin ruɗani, don haka a fadin ƙasar ake ta yin zanga zanga.
Mazauna birnin Goma da ya kasance helkwatar gabashin Kwango, suna cikin yanyin da ya yi muni matuƙa. Inda kemanin mutane 500 mata da yara ƙanana suke fake a bayan buhunan yashi da sojojin MDD suka jibgi. Mutane na zaune a kan ƙasa babu tabarma balle bargo, ga shi kuma ana yin yayyafin ruwan sama. Ana kuma jin tashin bindodgi nan da can a ɗaukacin daren. Dan haka wannan dattijo da matarsa da yaransa shidda suka fake bayan buhunan yashi na sojan MDD, inda yake ganin aƙalla kasancewar sa kusa da sojan na MDD yana jin wuta da yaransa shine mafi alheri a gare shi, inda ya ƙara da cewa.
"Lamarin a gaskiya yana da wahalar juriwa. babu magani, babu abinci, muna matuƙar tsoron makomar ruyawar yayan mu, wadanda tun ranar Lahdin ta gabata ba su ci komai ba. Harsasai da rokokin da ake harbawa sun yi ta wucewa ta kawu nan mu. Kai ko da anan wajen dakarun MDD ma bamu tsira ba. Wadannan kwanaki duk mun yi su ne a sararin Allah ta a'ala. Kai yanayin akwai firgitarwa"
A dai-dai lokacin da yan tawaye ke ta nausawa a bangaren da sojan gwamnati suke da iko. Har yanzu sai luguden wuta ake ji. Gabanin yan tawayen su kame birnin na Goma, sanda suka miƙa wa gwamnati buƙatar tattaunawa da kuma wa'adi na a yi hakan, amma shugaba Kabila yaƙiya. A lokacin kwamnadan yan tawayen M23 Innocent Kaina yace.
"Ya rage wa abokan gabanmu, idan sunce kuwa za su kai mana hari to za mu amshe iko da birnin Goma, domin muna da ƙarfin yin haka"
Daga ƙarshen dai bayan tsagaita wuta na watanni uku tsakanin sojan gwamnati da yan tawayen, barin wuta na kwanaki uku kacal ya sa yan tawaye M23 sun kame iko da birnin Goma.
Gabanin yan tawayen su kame birnin dai, kusan jama'a sun shirya, inda tsaffi suka fara tserewa matasa masu ƙarfi a jika wasu suka tsaya gaban gidajensu, yayinda wasu suka laɓe bayan bangwaye. Don haka ma yan tawayen cikin sauƙi suka kame birnin domin, sojan gwamnati sun arce. Don haka suka tarar da wadanda ke gadin gidajensu kawai dake jiran abinda zai wakkana.
Mawallafa: Simone Schidwein/ Usman Shehu Usman
Edita: Mohammad Nasiru Awal