′Yan Tawayen Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sun sake kwace gari | Labarai | DW | 29.12.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan Tawayen Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sun sake kwace gari

Duk da amincewa da shirin tattaunwa, a wannan Asabar kawance 'yan tawayen kasar ta Janhuriyar Afirka ta Tsakiya sun kwace garin Sibut

Duk da amincewa da shirin tattaunwa, a wannan Asabar kawance 'yan tawayen kasar ta Janhuriyar Afirka ta Tsakiya sun kwace garin Sibut, mai nisan kilo mita 150 daga Bangui babban birnin kasar, kamar yadda wasu majiyoyi da su ka nemi a sakaye sunansu su ka tabbatar.

A wani labarin kasar Faransa ta kara tura dakaru 150 zuwa kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, wadda ke fuskantar aiyukan 'yan tawaye, kamar yadda ma'aikatar tsaro da ke birnin Paris ta tabbatar.

Ma'aiktar ta ce an tura dakaru birnin Bangui domin kare Faransawa da sauran Turawa, kuma daga birnin Libreville na kasar Gabon aka tura su. Shugaban Faransa Francois Hollande ya kawar da yuwuwar dakarun na Faransa su taimakawa gwamnati Shugaba Francois Bozize, wanda ya shaida masa cewa lokaci ya kure.

Shugaba Bozize ya kwaci mafafun ikon kasar ta Jamahuriyar Afirka ta Tsakiya cikin shekara ta 2003, inda ya kifar da gwamnatin Ange-Felix Patasse, kuma dakarun Faransa sun cece shi, yayin tawayen shekara ta 2006, bayan ruwan wuta ta sama da ya karya lagon 'yan tawayen.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mohammadou Awal Balarabe