′Yan tawaye sun kwace fadar gwamnatin Yamen | Labarai | DW | 20.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan tawaye sun kwace fadar gwamnatin Yamen

Mayakan da ke biyayya ga kungiyar Huthi a kasar ta Yamen an tabbatar da cewa su ke iko da fadar shugaban kasar, bayan wani mummunan artabu da aka yi.

Rahotannin dake fitowa daga Sana'a babban birnin kasar Yemen, na nuni da cewa, mayakan Huthi, da ajiya suka yi yunkurin juyin mulki, a yau sun yi nasarar kame fadar shugaban kasar, bayan gumurzu da dakarun dake tsaron fadar sukayi da mayakan, artabun da yakai ga kashe biyu daga cikin masu tsaron shugaban kasar. Sai dai a cewar wakilinmu dake Gabas ta Tsakiya Mahmud Yaya Azare, har yanzu ba a samu bayanai kan halin da shugaban kasar, Abdu Rabbu Mansour Hadi yake ba.

"Dama dai, tun bayan da mayakan na Huthi suka mamaye babban birnin kasar Sana'a, a ranar 21 ga watan Satumba, shugaban yabar fadar ya koma gidansa, yadda yake gudanar da mulkin na sa daga can. Ministar yada labaran kasar Nadia Saqaff ta tabbatar da faduwar fadar shugaban kasa a hannun mayakan Huthi. Inda tace, a halin yanzu mayakan na Huthi na ci-gaba da wawaso a fadar. A nasu bangaren, kasashen Sarakunan yankin Gulf, da suka shiga tsakani don cimma yarjejeniyar zaman lafiyar, sun kira taron gaggawa, a gobe laraba a birnin Riyadh na Saudiya, don duba lamarin na kasar Yamen".

Daga nashi bangare, Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon, ya yi kira da a dakatar da gwabza fada a kasar, ta Yamen ba tare da wani bata lokaci ba.


Mawallafi: Salisou Boukari
Edita: Usman Shehu Usman