′Yan tawaye sun kai hari a Kwango | Labarai | DW | 08.08.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan tawaye sun kai hari a Kwango

'Yan tawayen kasar Ruwanda sun kashe mutane da dama da kona gidaje sama da dari a kauyukan Kibrizi da Kashila a arewacin Kwango.

'Yan tawayen kasar Ruwanda sun kai hari a wasu kauyuka biyu da ke arewacin kasar Kwanngo, jami'ai da kungiyoyin kare hakkin bil'Adama da ke kasar, sun bayyana wa kamfanin dillacin labarun DPA cewar 'yan tawayen Hutu ne 'yan asalin Ruwanda suka kai hari a kauyukan Kibrizi da Kashila inda suka yi sanadiyyar mutuwar mutane 17 ta hanyar bude wuta da bindigogi yayin da wasu ke harbi da kwari da baka da mashi.

Maharan sun kona gidaje sama da 100, to sai bayanai daga rundunar sojoji da ke ke lardin sun tabbatar da cewar sojoji sun yi nasarar hallaka maharan uku. A tun shekara ta 1996 zuwa shekara ta 2003 bayan yakin basassa a kasar Kwanngo, an samu bullar kungiyoyi masu fafutuka da makamai da ke kai hare-hare a kan fararen hula.