'Yan tawaye na kara samun galaba a rikicin Bangui
January 5, 2013Yayin da ya rage 'yan kawanaki kalilan a gudanar da tattaunawa tsakanin gwamnatin Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya da 'yan tawayen Seleka da ke kokarin ganin shugaba Francois Bozize ya kau daga karagar mulki, mazauna garin Alinda sun ce 'yan tawaye Seleka sun karbe iko da gari a wannan Asabar.
Da ya ke zantawa da manema labarai game da wannan batu, wani mazaunin garin Bangassou da ke kusa da garin na Alinda Jean Balipio ya ce 'yan tawaye sun kutsa kai a garin ne a tsakar daren jiya Juma'a, ba tare da fuskanci turjiya daga dakarun gwamnatin ba, inda su ka karbe iko da birnin.
Kame wannan gari na Alinda wanda shi ne cikon na sha daya da 'yan tawayen su ka kame, kuma hakan ya sanya shakku ga zukatan al'ummar kasar da ma masu shiga tsakani a rikicin, dangane da fatan samun sararin warware takaddamar da ke tsakanin 'yan tawayen na Seleka da kuma shugaban kasar ta Jamhuriyar Afrika ta tsakiya.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Usman Shehu Usman