1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan tawaye a Kongo na ƙara samun galaba a gabacin ƙasar

November 22, 2012

Mutane kimanin dubu 10 sun samu nasarar tsere wa daga faɗan da ake yi tsakanin 'yan tawayen M23 da kuma dakarun gwamnati.

https://p.dw.com/p/16oMU
Hoto: picture-alliance/dpa

'Yan tawayen ƙungiyar M23 a jamhuriyar demokraɗiyyar Kongo na ƙara dannawa birnin Bukavu mai muhimmanci dake gabacin ƙasar. Bayan da a cikin wannan makon suka ƙwace iko da biranen Goma da Sake, faɗuwar birnin Bukavu ka iya zama babbar nasara ga 'yan tawayen a cikin shekaru 10 da suka gabata. Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi ƙiyasuin cewa mutane kimanin dubu 10 sun samu nasarar tsere wa daga faɗan tsakanin 'yan tawayen na M23 da kuma dakarun gwamnati. A garin Goma dubban sojoji da 'yan sanda sun mika kansu ga 'yan tawayen waɗanda suka lashi takobin kifar da gwamnatin shugaba Josef Kabila. Jenerali Ulimwengu, fitaccen ɗan jarida ne a ƙasar Tanzania, kana mai yin sharhi a kan harkokin siyasa ya ce 'yan tawayen na fuskantar dakarun gwamnatin da ba su da cikakken tsari. "Abinda yake a zahiri dai shi ne cewar babu dakarun dake yin biyayya ga hukumomi a birnin Kinshasa a wannan yankin. 'Yan tawayen ba sa fuskantar wata turjiya, lamarin da ya sa suke yin abinda suka ga dama kawai."

Ana zargin ƙasashen Uganda da Ruwanda da taimaka wa 'yan tawayen da makamai, yayin da ƙungiyoyin agaji kuma suka ce ana ɗaukar ƙananan yara aikin soji a yankin.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Usman Shehu Usman