1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwango: 'Yan takara sama da 20 ke fafatawa

Abdul-raheem Hassan
September 19, 2018

Sama da 'yan takara 20 ne suka yi rejista a hukumar zabe na Jamhuriyyar Dimukuradiyyar Kwango CENI. Sai dai bisa ga dukkan alamu, matsayin dan takarar Shugaba Joseph Kabila na da tasirin a zaben da ke tafe.

https://p.dw.com/p/35BMB
Kongo Emmanuel Ramazani Shadary
Hoto: REUTERS

Za dai a iya cewa Shugaba Joseph Kabila, ya yi kyakkyawar taku bayan sanar da matakinsa na janye aniyarsa ta sake takarar shugabancin kasar karo na uku. A kan haka ya zakulo tsohon ministan harkokin cikin gida a gwamnatinsa Emmanuel Ramazani Shadary cikin 'yan takarar gadon kujerar shugabancin kasar.

Sai dai masana kamar Gesine Ames na cibiyar Ecumenical Network a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, na ganin dan takara Shadary ba shi da tasiri a jam'iyya mai mulki, amma yadda yake zama karen farautar Joseph Kabila, ko da ya ci zabe tamkar rakumi ne da akala a hannun Shugaban.

"Za a zabe shi ne ko dai zai maye gurbin kujerar, zai dai ci gajiyar abokantakarsu da Shugaba Kabila"

Kuri'ar ra'ayin jama'a dai bai nuna alamun nasara kan dan takarar jam'iyyar PPRD mai shekaru 57 da Shugaba Kabila ke marawa baya ba.

A yanzu haka dai Emmanuel Ramazani Shadary na cikin takunkumin kungiyar Tarayyar Turai kan zargin cin zarafin bil'adama a yankin Kasai, bugu da kari dai ana ganin dankarar bai da sanayya cikin kasar.

Sabbin dokokin hukumar zaben kasar Jamhuriyyar Dimukuradiyyar Kwango, sun bukaci ko wane dan takarar kujerar shugaban kasa da ya samu rinjaye mafi karanci kamin yin nasara, abin da ke zama karfen kafa hatta jam'iyyun adawa da ke da 'yan takara masu cike da sarkakiya.

Felix Tshisekedi da Vital Kamerhe na cikin 'Yan takara 19 suka yi fice, sai dai hukumar zaben kasar CENI ta haramta wa 'yan takara biyu na jam'iyyun adawa Jean-Pierre Bemba da Moise Katumbi da sunayensu ke farko farko a jerin sunayen 'yan takarar shugaban kasar ta Kwango yin takara.