1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan ta'adda sun kashe sojoji a Mali

Abdul-raheem Hassan MAB
March 17, 2019

Wasu maharan cikin manyan motoci da babura sun kai hari a cikin sansanin sojojin kasar Mali da ke garin Diouri, inda suka bude wuta kan sojoji da ke aikin tabbatar da tsaro a yankin.

https://p.dw.com/p/3FD5k
Bildergalerie Kriege im Jahr 2013
Hoto: picture-alliance/dpa

Wasu 'yan bindiga da ake zargin 'yan ta'adda ne sun kashe sojoji takwas a wani hari kan sansanin sojoji da ke tsakiyar kasar Mali. Sai dai akwai fargabar adadin mutuwar ya karu. Rundunar sojin kasar Mali ta ce sojojin sun fafata da 'yan ta'addan da suka kaddamar da harin.

Kasar Mali ta fuskanci hare-hare akalla 237 a shekarar 2018 duk da cewa akwai rundunar kiyaye zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a Mali da sojojin Faransa hada da rundunar sojojin hadin gwiwa na kasashen yankin Sahel.