′Yan sandan Masar sun kashe ′yan bindiga | Labarai | DW | 24.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan sandan Masar sun kashe 'yan bindiga

'Yan sandan Masar sun dauki fansa a kan 'yan bindiga da ake zargi da yawan kai hare-haren ta'addanci a yankin Sinai inda suka yi nasarar kashe mutane tara daga cikin 'yan ta'addan.

Rundunar 'yan sandan Masa ta tabbatar da kashe wasu 'yan bindiga tara da ake zargi da kitsa kai hare-hare a yankin Sinai da ke Arewa maso gabashin kasar. Ma'aikatar cikin gidan kasar ta ce sumamen ya biyo bayan samun labarin cewar 'yan ta'addan sun kafa sansanin horars da makaman yaki a lardin Sharqiya. 'Yan sanda sun kuma gano manyan bindigogi masu sarrafa kansu da sinadaran sarrafa bama-bamai a sansanin 'yan ta'addan.

Dama dai ana zargin gungun 'yan bindiga da suka tare a gandun dajin Sharqiya da alhakin hare-hare a kan ofisoshin 'yan sanda da jami'an soji, wadanda suka yi sanadiyyar mutuwar jami'an tsaro da dama a yankin Sinai.

Tun dai bayan wani mummunan hari da ya kashe mutane sama da 300 a masallacin Jumma'a watannin baya, Shugaban kasar Masar Abdel Fatah al-Sisi ya umarci jami'an tsaro da su murkushe ayyukan ta'addanci a kasar cikin watanni uku.