1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Jigon adawa a Guinea ya kai kansa wurin 'yan sanda

November 14, 2020

Wani fitaccen dan adawa a siyasar kasar Guinea Cellou Balde ya kai kansa ga 'yan sanda a ranar Jumma'a.

https://p.dw.com/p/3lHtX
Guinea Politiker Cellou Dalein Diallo
Hoto: picture-alliance/dpa/Maxppp/S. Souici

Wani fitaccen dan adawa a siyasar kasar Guinea Cellou Balde ya kai kansa ga 'yan sanda a ranar Jumma'a. Balde dai ya yanke shawarar hakan ne bayan da rundunar 'yan sandan kasar ta sanar da shi a cikin mutanen da take nema ruwa-ijallo. A yanzu Balde ya shiga cikin wasu jagororin adawa hudu da hukumomin Guinea ke tsare da su a cikin wannan makon. 

'Yan sandan sun bayar da sanarwar neman jiga-jigan adawar su biyar bayan artabun da aka yi tsakanin jami'an tsaro da magoya bayan 'yan adawa jim kadan bayan zaben shugaban kasar ta Guinea da aka gudanar a ranar 18 ga watan da ya gabata.

Kimanin mutum 21 ne aka ce sun rasa rayukansu a wurin yin adawa da lashe zaben Shugaba Alpha Conde a wa'adi na uku. Rikicin bayan zaben ya kaure ne jim kadan bayan da dan takarar jam'iyyar adawa ta UFDG Cellou Dalein Diallo mai shekaru 68 yayi zargin shi ne ya lashe zaben na Guinea amma Shugaba Alpha Conde ya murde.