′Yan sandan Amirka sun kama wanda ake zargi da tayar da bam | Labarai | DW | 20.04.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan sandan Amirka sun kama wanda ake zargi da tayar da bam

An cafke wanda ake zargi da kai harin bam yayin gudun yada kanin wani na garin Boston na Amirka

An cafke wanda ake zargi da kai harin bam yayin gudun yada kanin wani na garin Boston da ke Jihar Massachusetts ta kasar Amirka. An kama shi bayan harbe harbe da 'yan sanda, kuma yanzu ya na asibiti, wajen da ake masa jinya saboda raunukan da ya samu.

Dan shekaru 19 da haihuwa Dzhokhar Tsarnaev, an kama shi a yankin da ke Boston. Dan uwansa da ake zargin su tare Tamerlan Tsarnaev, dan shekaru 26 da haihuwa ya hallaka, yayin da ya yi yunkurin tserewa 'yan sanda cikin daren Alhamis zuwa wayewar garin Jumma'a.

Harin da ake zargin mutanen 'yan asalin yankin Chechiniya na kasar Rasha da kaiwa, wadanda sun dade zaune cikin Amirka, ya yi sanadiyar hallaka mutane uku da jikata wasu 170.

Jim kadan bayan 'yan sanda sun kammala aikin, wanda ya janyo dillace daukacin garin, Shugaban kasar ta Amirka Barack Obama ya gudanar da jawabi, wanda ya ce za a gudanar da bincike tabbatar da sanin dalilan da su ka janyo harin na ta'addanci.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Thomas Mösch