1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yan adawa a Ghana sun yi zanga-zanga

Abdourahamane Hassane
December 17, 2020

'Yan sanda a birnin Accra na Ghana sun yi amfani da kulake da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa wasu darurruwan jama'ar magoya bayan 'yan adawa da suka yi zanga-zanga a kusa da ginin hukumar zabe.

https://p.dw.com/p/3mssu
Ghana | Präsidentschaftswahlen
Hoto: Pius Utomi Ekpei/AFP/Getty Images

'Yan adawar sun yi gangamin ne domin nuna kin amincewa da sakamakon zaben da hukumar ta bayyana wanda ta tabbatar cewa Nana Akufo Addo shi ne ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar tara ga watan Disamba, da kishi 51,59 a gaban dan takarar jam'iyyar adawa John Mahama da ke dashi 47.36. Jami'an tsaron na Ghana sun kama da yawa daga cikin shugabannin adawar da suka jagoranci gangamin.