′Yan sanda sun kai samame a birnin Tunis | Labarai | DW | 24.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan sanda sun kai samame a birnin Tunis

Rohotanni daga birnin Tunis na kasar Tunisiya na cewa, a kalla mutane shidda ne suka rasu yayin wani samame da jami'an tsaron 'yan sanda suka kai ga wasu yan ta'adda.

Jami'an tsaron sun kai samaman ne a wani gida dake yammacin birnin na Tunis, inda wasu masu dauke da makammai suka yi garkuwa da mutane da dama. Tun farko dai 'yan sanda dake jagorancin tattaunawa da 'yan ta'addar, sunyi kokarin samun walwale wannan matsala ta ruwan sanyi, amma duk da haka aka samu kai wannan samame da yayi sanadiyar mutuwar mata biyar da namiji daya, wanda a cewar kakakin ofishin ministan cikin gidan kasar ta Tunisiya, daya daga cikin matan ce ta fara buda wuta ga jami'an tsaron. A ranar Lahadi ce dai mai zuwa za'a gudanar da zaben 'yan Majalisun dokoki a wannan kasa, sai dai kuma tun a wannan Juma'ar 'yan kasar ta Tunisiya dake kasar Faransa sun soma zaben.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Pinado Abdu Waba