1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kubutar da mutanen da aka sace a Texas

Abdul-raheem Hassan
January 16, 2022

Hukumomin tsaro sun yi amfani da dabarun aiki wajen shawo kan mai garukuwa da mutane don kubutar da mutane hudu da ya sace a cikin wata majami'a a birnin Texas.

https://p.dw.com/p/45b5r
Amirka | Texas | Garkuwa da mutane
'Yan sanda a wajen harabar da aka yi garkuwa da mutane a TexasHoto: Tony Gutierrez/AP Photo/picture alliance

Jami'an tsaro a Amirka sun tabbatar da kwato dukkannin mutane 4 da wani dan bindiga ya yi garkuwa da su tsawon sa'a 10 a wata majami'a a jihar Texas, hukumomin sun cimma kubutar da mutanen ba tare da waniya  mutu ba a cikinsu.

Gidan talabijin na ABC ta ruwaito cewa dan bindigar ya ji rauni, har ma ya tarwatsa kansa a wani wuri da ba a sani ba. Matthew DeSarno, wakili na musamman da ke kula da ofishin Bincike na tarayya a Dallas ya ce za su kaddamar da bincike kan lamarin."Babu karin bayani da ke nuna cewa wannan lamari zai zama barazana, amma dai wanda ya yi garkuwan ya mutu. Kuma za mu gudanar da bincike mai zaman kansa, tawagar masu bincike za ta zo aiki nan daga Washington don gano karin bayani kan ainihin abin da ya faru."