′Yan sanda sun buɗe wuta a kan masu bore a Burkina | Labarai | DW | 30.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan sanda sun buɗe wuta a kan masu bore a Burkina

Rahotannin da ke zuwa mana daga Burkina Faso na cewar jami'an tsaro sun buɗe wuta a kan daubban jama'a masu zanga- zanga a lokacin da suke ƙoƙarin danawa fadar shugaban ƙasar.

Tun farko masu yin boren sun ƙone ginin majalisar dokokin ƙasar a yau,a dai dai lokacin da aka shirya majalisar za ta tattauna ƙudirin bai wa shugab Blaise Compaore damar yin takara a a zaɓen shugaban ƙasar wa'adi na biyar.

Sannan kuma a garin Bobo Dioulasso, birnin na biyu mafi girma na ƙasar an ba da rahoton cewar an ƙone ofishin magajin garin birnin da kuma cibiyar jam'iyyar da ke yin mulki.