′Yan sanda na tsare da wasu ′yan jarida a Nijar | Labarai | DW | 26.01.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan sanda na tsare da wasu 'yan jarida a Nijar

Gwamnatin na zargin 'yan jaridar da yunƙurin kawo fitina a cikin ƙasar da kuma wasu 'yan siyasa.

Haɗin gwiwar ƙungiyoyin 'yan jaridu masu zaman kansu, sun bayyana wata sanarwa domin yin Allah wadai da matakin da gwamnatin ta ɗauka na kama wasu 'yan jaridun.

'Yan jaridun, waɗanda suka haɗa da Soumana Idrissa Maiga,Editan wata jarida mai zaman kanta, ta Enquetteur,da Abdullahi Maman, ɗan jaridan wani gidan talbijan mai zaman kansa Bonferey, kuma wakilin Muryar Amirka a Nijar. An kama su ne a kan zargin da gwamnatin ta ke yi musu na wallafa wasu bayanai da kuma yin muhawara da suka ce lamarin na iya kawo tashin hankali.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Saleh Umar Saleh