1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan Rohinga na tserewa daga sansaninsu

Gazali Abdou Tasawa
November 13, 2018

Daruruwan Musulmi 'yan kabilar Rohinga na kasar Myanmar da ke zaman gudun hijira a Bangladash na tserewa daga sansanoninsu a daidai lokacin da gwamnatin ta Bangladash ke shirin soma aiki mayar da su kasarsu ta asali.

https://p.dw.com/p/38A47
Bangladesch Myanmar - Grenzgebiet Rohingya - Flüchtlinge
Hoto: Getty Images/AFP/T. Mustafa

Rahotanni daga kasar Bangladash na cewa daruruwan Musulmi 'yan kabilar Rohinga na kasar Myanmar da ke zaman gudun hijira a kasar ta Bangladash na tserewa daga sansanoninsu a daidai lokacin da gwamnatin ta Bangladash ke shirin a wannan mako soma aiki mayar da su kasarsu ta asali. 

Gwamnatin ta Bangladesh na shirin soma mayar da 'yan Kabilar Rohingan ne a kasarsu a karkashin wata yarjejeniya da ta cimma da gwamnatin kasar ta Myammar wacce ta tanadi mayar da 'yan Rohingan dubu biyu da 260 zuwa gida daga ranar 15 ga wannan wata na Nowamba. 

Sai Shugabannin 'yan kabilar ta Rohinga a Bangladash sun ce da dama daga cikin iyalan da aka yi rijistansu domin mayar da su kasar tasu sun tsere daga sansanoninsu a bisa tsoron abin da ka iya faruwa a gare su idan sun koma gida. Da ma dai Majalisar Dinkin Duniya ta ce babu wani gamsasshen shiri da gwamnatin ta Myanmar ta yi domin sake karbar 'yan kabilar ta Rohingas a kasar.