1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan mata na ganin tasku a wurin yaki

Yusuf Bala Nayaya
September 24, 2018

Yara kanana mata na kan gaba wajen ganin gallazawa da cin zarafi da tilasta masu auren wuri da hana masu 'yancin karatu idan aka kwatanta da takwarorinsu maza, a cewar rahoton Plan International.

https://p.dw.com/p/35Nn7
Manuela - Flucht aus dem Südsudan in die Dürre
Hoto: DW/S. Petersmann

Wannan matsala na zama gagaruma a yankunan da ake fama da tashe-tashen hankula a cewar rahoton da wata kungiya mai zamana kanta ta kasa da kasa Plan International ta fitar a ranar Lahadi.

A wannan Litinin kuma a zaman taron Majalisar Dinkin Duniya kungiyar za ta fitar da wasu bincike uku da ta gudanar kan makomar manyan na gobe a tsakanin al'ummar Rohingya na Myanmar da ke samun mafaka a Bangaladash. Sai rahoto na biyu da ya shafi matsalolin rayuwa a yankin Tafkin Chadi da kuma rahoto na uku kan Sudan ta Kudu, yankuna uku da zaman lafiya ya gagara samuwa.

Har ila yau binciken ya kuma gano tilasta auren wurin da cin zarafi da aikata fyade da bautarwa da rashin samun ilimi a sansanoni da suka tumbatsa a Yuganda bayan da kungiyar ta tattauna da wasu 'yan mata kusan 250 wadanda ke shekaru tsakanin goma zuwa 19, 'yan matan da ke zama 'yan asalin Sudan ta Kudu.