1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

'Yan majalisar dokokin Amurka sun kasa tsawaita kasafin kudi

Mouhamadou Awal Balarabe
September 19, 2024

Fiye da 'yan Republican 12 sun bi sahun 'yan Democrat wajen kin amincewa da tsawaita kasafin kudin har zuwa Maris 2025, matakin da ke iya haddasa tafiyar hawainiya ga harkokin tafiyar da gwamnatin gabanin zaben Nuwamba.

https://p.dw.com/p/4kolG
'Yan majalisar Amurka sun yi burus da batun tsawaita kasafin kudin bana
'Yan majalisar Amurka sun yi burus da batun tsawaita kasafin kudin banaHoto: Liu Jie/Xinhua/picture alliance

 Bisa ga tsarin kasar Amurka, wajibi ne majalisun wakilai da na dattawa su amince da kasafin 2025 a karshen Satumba, idan ba haka ba miliyoyin ma'aikatan gwamnati na iya rasa aikinsu yayin da a daya bangaren za a dakatar da taimako ga marasa galihu da ma dai zirga-zirgar wasu jiragen sama sakamkon rashin kudi. Fiye da 'yan jam'iyyar Republican 12 ne suka bi sahun 'yan jam'iyyar Democrat wajen kin amince da tsawaita kasafin kudin har zuwa watan Maris na shekarar 2025, wato har bayan dan takarar da aka zaba a zaben shugaban kasa na ranar 5 ga watan Nuwamba ya hau kan karagar mulki.

Karin bayani:An cimma matsaya kan kasafin kudin Amurka 

Dama dai dan takarar jam'iyyar Republican Donald Trump ya yi barazanar kawo tseko a matakin tsawaita kasafin kudin Amurka, matikar da ba a yi amfani da wannan dama wajen amincewa da kudirin dokar nuna shaidar zama dan kasa lokacin kada kuri'a ba. Sai dai gwamnatin Joe Biden na adawa da wannan mataki, tana mai cewa babu wata shaida da ke nuna cewa baki za su iya taka rawa a zabe mai zuwa.