Uganda na musgunawa 'yan jaridu
January 11, 2016Talla
Zargin dai na zuwane a dai-dai lokacin da ake gab da fara zaben shugabancin kasar a wata mai kamawa.
'Yan takarar shugabancin kasar bakwai ne dai suke kokarin bugawa da Shugaban kasar mai ci Yoweri Museveni da ya shafe shekaru 30 a gadon mulki a ranar 18 ga watan Febreru, a yayin da ake fargabar barkewar rikici a lokutan yakin neman zaben sakamakon sukar lamirin juna kan cin hanci da karbar rashawa a tsakanin 'yan takarar.
Kazalika kungiyar tace gwamnati ta dakatar da wasu aikace -aikacen 'yan jarida tare barazanar daukar matakai masu tsauri ga gidajen radiyon kasar muddin suka dauki nauyin watsa shirye-shiryen 'yan adawar kasar.