Matsalar musguna wa 'yan jarida na karuwa
December 9, 2021Talla
Kwamitin kare hakkin 'yan jarida na(CPJ) ya sheda halin tasku da 'yan jarida da dama ke ciki a sassan duniya, a rahoton kwamitin na wannan Alhamis, ya ce, alkaluman yawan 'yan jarida da ake tsare da su a gidajen yari saboda kawai suna gudanar da ayyukansu ya haura sosai inda aka samu karin da ya zarta kima a cikin wannan shekarar ta 2021 mai karewa.
Kididdiga na shekara-shekara na CPJ ya hada dana 'yan jarida da aka daure ko aka kashe su a sassan duniya. Daga bara ya zuwa yanzu, akalla 'yan jarida 280 ne suka samu kansu a gidan kurkuku a yayin da kimanin 'yan jarida 24 ne suka mutu a bakin aiki. Kasar Chaina ce a sahun gaba daga cikin kasashen duniya da aka fi musgunawa dama daure 'yan jarida.