′Yan jarida na fiskantar barazanar tsaro a Bangui | Zamantakewa | DW | 14.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

'Yan jarida na fiskantar barazanar tsaro a Bangui

Camille Lepage ita ce 'yar jarida na baya-bayan nan da ta rasa ranta a Bangui, kuma ana korafin gwamnati ba ta daukar mataki wajen kare su ko kuma hukunta masu aikata wannan aiki

Har yanzu dai akwai matsalar tsaro a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, inda duk da kasancewar dakarun sojin Turan da suke tallafawa wajen tabbatar da tsaro, ana cigaba da samun rahotannin tashe-tashen hankula, kuma 'yan jarida a kasar na fiskantar barazanar rasa rayuwarsu. Na baya-bayan nan dai shi ne kissan gillar da aka yi wa Camille Lepage wata 'yar jarida, 'yar asalin Faransa mai shekaru 26 na haihuwa.

An gano gawar Camille Lepage ne a Bouar, wani birni da ke da tazarar kilometa 450 daga arewa maso yammacin Bangui, kusa da iyakar kasar da Kamaru. Wasu dakarun sojin Faransar da aka fi sani da "Sangaris" ne suka gano gawar a bayan wata mota kirar akori kura, wanda ake kyautata zaton cewa 'yan tawayen kugiyar anti Balaka ne suka tuka ta. Kawo yanzu dai dakarun sun ce babu cikakken bayani kan dalilai, ko kuma ma yadda aka yi aka kai ga kissar watan mata.

Bildergalerie Camille Lepage Screenshot Twitter

Shafin Lepage na Twitter

Lokacin da ya ke ziyar a Tiblisi babban birnin kasar Georgiya, shugaban kasar Faransa Francois Hollande, ya ce ya ba da gaskiya Lepage tana aikinta ne na daukar hoto, ta fada hannun wadannan mutane

Lepage tana aiki ne a matsayin 'yar jarida mai daukar hoto da kamfanin Hans Lucas, wanda ke da shelkwatarsa a birnin Paris, kamar yadda ya bayyana a shafin shi na yanar gizo.

Wannan mutuwa na ta na zuwa ne bayan watanni shidda da mutuwar wasu ma'akatan gidan rediyon Farance na RFI a kasar mali

'Yan jarida sun fara barin aikinsu sakamakon barazana

Wannan mutuwa ta Camille Lepage, ya sanya ta cikin jerin 'yan jaridan da aka kashe a kasar ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Daga farkon watan Mayu, an hallaka wasu 'yan jaridan kasar guda biyu. Wannan batu dai ya sanya ma'aikata da dama na fanin sadarwa barin ayyukansu, kamar dai yadda wannan dan jaridan, wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya bayyana:

"Da zarar ka yi suka, rayuwarka za ta shiga cikin hatsari. Muna fuskantar barazanar tsaro. Ran kaza ya fi na dan Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, domin gwamnati ba ta daukan matakai na biyan diyya, ba a gurfanar da wadanda suka aikata laifi gaban kuliya. Mu dai Allah ne mai karemu."

Ba wanda ke da 'yancin walwala bare na fadin albarkacin baki

Kamar dai yadda ya bayyana, matsalar na cigaba da ta'azara a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiyar, mutane 13 sun rasa rayukansu jiya a garin Dikissou wanda ke da can yankin arewacin kasar, wanda ba shi da nisa da iyakar kasar da Chadi. Mgr Nestor Désiré Nongo-Aziagbia, wanda shi ne babban Bishop na Bossangoa ya ce bai fahimci dalilin da ya sa har yanzu ake fama da wannan matsalar tsaron ba.

"Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya wani gidan yari ne da ba shi da kofa, domin ba me da 'yancin fadan albarkacin baki, ba me cikakken 'yancin walwala. Wai shi wani mataki aka dauka domin ganin an kwace bindigogi a hannun mayakan sa kai kamar yadda kudirin Majalisar Dinkin Duniya ya tanada? tambayar da kowa ya ke dasawa ke nan, tambayar da har yanzu ba ta da amsa."

Zentralafrikanische Republik Unruhen 26.02.2014

Daya daga cikin irin hotunan da Lepage ta dauka

Tuni dai Majalisar Dinkin Duniya ta aikar da sakon ta'aziyyar ta ga 'yan uwa da abokan arzikin Lepage, tana mai jaddada cewa, a duk yankunan da ke fama da rikici, ya kamata a dauki 'yan jarida a matsayin fararen hula. Haka nan kuma a wata sanarwar da ta turawa gwamnatin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiyar, Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci da a gudanar da bincike dan gano musabbabin wannan aikin asha, ya kuma ce wajibi ne a hukunta su.

Ranar Talata, shugaban Amirka Barack Obama ya sanya takunkumi kan tsoffin shugabanin kasar biyu, Francois Bozize da Michel Djotodia da wasu manyan jami'ai uku. kuma wannan na zuwa ne bayan da ita Majalisar Dinkin Duniya ta kakabawa mutanen biyar irin wannan takunkumin ranar juma'ar da ta gabata

Mawallafiya: Pinado Abdu Waba

Edita: Abdourahamane Hassane