′Yan jarida mata na fuskantar barazana | Labarai | DW | 05.03.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan jarida mata na fuskantar barazana

Kungiyar 'yan jaridu ta kasa da kasa Reporters Without Borders (RSF) ta ce 'yan jaridu mata na fuskantar barazanar kisa da hukuba da kuma dauri a gidajen kurkuku a cikin wasu kasashen duniya.

A cikin wani rahoton da ta bayyana daf da lokacin da ake shirin gudanar da bikin ranar mata ta duniya ran takwas ga watan Maris. Kungiyar ta RSF ta ce tsakanin shekara ta 2016 da 2017 an kiesta kamar mata 60 a cikin kasashe 20 wadanda suka samu kansu cikin irin wannan hali saboda aikin da suke yi na bincike kan halin rayuwar mata. Kassahen China da Masar da Turkiyya na daga cikin kasashen da matan 'yan jarida ke fuskantar galazawa.