′Yan gudun hijirar Tigray na samun taimako | Labarai | DW | 27.11.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan gudun hijirar Tigray na samun taimako

Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da tan 30 na kayayakin agaji aka kai Khartum domin taimaka wa dubban 'yan gudun hijirar kasar Habasha da suka tserewa rikicin yankin Tigray.

Hukumar 'yan gudun hijira ta MDD na fatan samun karin kayayyakin agajin daga Hadaddiyar Daular Larabawa a ranar Litinin mai zuwa.

Mai magana da yawun hukumar 'yan gudun hijira Babar Baloch ya ce suna ci gaba da neman taimako don tallafa wa 'yan gudun hijirar Habasha wanda ya ce mafi yawancinsu mata ne da kananan yara.

A jiya Alhamis, Firamnistan kasar Abiy Ahmed ya ba da umurnin far wa mayakan yankin Tigray jim kadan bayan cikar wa'adin kwanaki uku da ya bai wa 'yan awaren na mika wuya.