′Yan gudun hijira na so a yi zabe da su a Najeriya | Siyasa | DW | 03.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

'Yan gudun hijira na so a yi zabe da su a Najeriya

Makomar dubban ‘yan gudun hijirar da ke zube a sassan jihohin arewacin Najeriya, sanadiyyar matsalar tsaro ka iya kasancewa kalubale a zabuka masu zuwa

Tun lokacin da hukumar zaben Najeriya ta ankarar da cewa da yawan 'yan gudun hijirar da ake da su, matukar ba su samu damar yin zabe ba, to kuwa akwai yiwuwar samu matsala bayan zaben musamman idan aka kalubalanci lamarin a gaban kotu. Majalisar dokokin Najeriya cikin gaggawa ta samar da kudirin da zai baiwa ‘yan gudun hijirar damar yin zabe a wuraren da suke tare da sabunta katunan zabe ga wadan da ba su da katin zaben.

Wannan mataki ya farantawa yawancin ‘yan gudun hijirar da suka zaku su yi zaben shugabannin da suka yi imani za su fitar da su daga kangin da suke ciki. Da dama dai sun samu wannan katin zabe inda wasu kuma har ya zuwa yanzu ba a kai samun katunan na su ba. Malam Ammar Alkali Dahiru daya daga cikin wadan suka samu katin zaben su ne ya kuma shaidawa DW cewa shi kam da sauran 'yan uwan sa zasu yi zabe.

Thema - Binnenflüchtline in Nigeria

Mutane sama da milliyan guda ake kyautata zaton sun rasa matsugunnensu

To sai dai duk da wannan zakuwa na yin zabe da wadannan ‘yan gudun hijira suka yi matukar ba su koma jihohin na asali a wuraren da aka tanada musu ba, to kuwa ba zasu samu damar yin wannan zabe ba bisa tsarin da hukumar zabe ta kasa ta yi. Barr Kassim Gaidam shi ne kwamishinan Hukumar Zabe mai cin gashin kanta ta kasa a jihar Gombe wanda ya tabbatar da wannan matsayi na hukumar inda ya bukaci ‘yan gudun hijirar su kuma jihohinsu na asali wuraren da aka tanada in suna son yin zabe.

Babban abin damuwa a nan dai shi ne akwai ‘yan gudun hijirar da har yanzu hukumomi ba su kai ga sanin wuraren da suke ba inda wasu kuma ba su samu kwanciyar hankalin da zai sa su iya samun sukuni na yin zaben ba.

Sauti da bidiyo akan labarin