'Yan gudun hijira a Muzambik na bukatar agaji
July 6, 2021Talla
Sama da mutun 730,000 ne ke cikin hatsarin afkawa cikin matsanancin karacin cimaka a yankin, ma damar ba a kai masu daukin gaggawa ba, ta bakin daraktan hukumar abinci na majalisar David Beasley bayan wata ziyarar gani da ido da ya kai a yankin.
Yankin na Cabo Delgado mai arzikin iskar gas ya kasance cikin rikici tun a shekara ta 2017 lokacin da masu ikirarin jihadi suka fara kai hare-haren ta'adanci da suka hallaka al'umma da dama wasu kuma suka tsallake matsugunnansu.