′Yan fashin ruwan teku sun kai hari ga wani jirgin ruwa a Najeriya | Labarai | DW | 24.12.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan fashin ruwan teku sun kai hari ga wani jirgin ruwa a Najeriya

Sama da shekaru goma kenan da ruwan tekun kudancin Najeriya ya soma zama wani dandalin 'yan fashi duk kwa da matakan da hukumomin ƙasar ke ɗauka.

default

'Yan fashin ruwan teku a Najeriya

Hukumar kula da zirga-zirgan jiragen ruwa ta ƙasa da ƙasa ta bayana cewar wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wane ba,sun kaiwa wani jirgin ruwa mai sufirin man fetur hari a kudancin Najeriya,inda kai tsaye suka yi awon gaba da wasu turawa guda huɗu da ke cikinsa. Ko da yake rahotani daga kamfanin dillancin labaran Faransa da ya ruwaito wannan labarin,ya ce duk da harin da aka kai masa,jirgin ruwan ya samu nasarar kaiwa wata mashigar ruwa inda ya samu tsira. Tuni dai masu nazarin al'amura ke nuna fargaban ganin kudancin Najeriyar ya kasance wani sabon filin daga ruwan teku,ƙasasr da ke yawan fuskantar wannan matsalar.

Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Yahouza Sadissou Madobi