′Yan Cote d′Ivoire sun amince da kudin tsarin mulki | Siyasa | DW | 02.11.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

'Yan Cote d'Ivoire sun amince da kudin tsarin mulki

Al'umma ta kada kuri'ar amincewa da gaggaurimin rinjaye da yin kwaskwarima ga kudin tsarin mulkin kasar bayan wata kuri'ar raba gardama da aka gudanar a ranar Lahadin da ta gabata.

Sabon kudin tsarin mulki wanda shugaba Alassane Ouattara ya gabatar da shi zai ba da damar kawo karshen srakakiyar siyasar kasar da aka kwashe sama da shekaru goma ana yin tankiya a kai tsakanin sojoji da 'yan siysasa, a game da batun wanda a cancanci yin takara kana a zabeshi.Sannan sabon kudin tsarin mulkin ya tanadi zabar majalisar dattawa, da mataimakin shugaban kasa da kuma majalisar sarakunan gargajiya,Maria Ange na daya daga cikin magoya bayan jam'iyyun siyasar da ke goyon bayan sabon kudin tsarin mulkin

Ta ce : ''Lokacin da dukkanin shugabanninmu suka halarci taron kasa su dukkaninsu Affi Nguessan da Alassane Outtara da Guillaume Soro tare su, suka yanke shawara a sake duba kudin tsarin mulkin kasar saboda akwai kura-kurai a ciki wadanda suka janyo mana yaki a baya.

Sabon kudin tsarin mulkin dai ya samu amincewar jama'a da kishi 93 cikin dari na kuri'un da aka kada yayin da yawan wadanda suka fito don yin zaben ya kai kishi 42.da digo 42.'Yan adawa sun kauracewa kada kuri'ar bayan da suka ce gwamnatin ba ta tuntubesu ba,haka ma kungiyoyin farar hula wadanda kuma suka ce yin haka wata babbar murdiya ce da za ta mayar da kasar baya.

A shekarun baya dai masu yin adawa da Alassane Ouattara sun rika yi masa  zargin cewar ba dan kasa ba ne, asilinsa Burkina Faso abin da ya sa a tsawon shekaru da dama ya gaza tsayawa takara a zaben shugaban kasar kafin daga baya ya samu mulki.Kwame Ajoumani shugaban kungiyar kare hakin bil Adama na Cote d'Ivoire ya ce zaben na raba gardama an yi shi da kura-kurai.

Ya ce ''tsarin da aka yi na zaben na kuri'a daya muna gani abu ne da aka aminta da shi amma kuma daga bisani ba a yi aiki da shi ba, sai aka yi aiki da tsarin kuri'u da yawa abin da ya sa aka samu rudami annan koma baya ga sha'anin demokaradiyya''

A yanzu da wannan sabon kudin tsarin mulki shugaba Ouattara na iya nada mataimakin shugaban kasa har zuwa shekara ta 2020, kuma wasu masu yin sharhi na cewar shugaban na iya fuskantar mummunar adwa idan har ya nemi ya yi takara  a karshen wa'adin mulkinsa.

 

 

Sauti da bidiyo akan labarin