′Yan bindiga sun kashe sojojin Mali | Labarai | DW | 28.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan bindiga sun kashe sojojin Mali

Wasu 'yan bindiga sun hallaka sojin kasar Mali guda uku lokacin da suka kai musu farmaki a wani sansani da suke aiki a Meneka da ke kan iyakar kasar da Jamhuriyar Nijar.

Masu aiko da rahotanni suka ce 'yan bindigar sun yi dirar a wajen ne a yau (28.01.2018) kafin gari ya kammala wayewa idan suka yi wa wajen kawanya kana suka fara har irin na kan mai tsautsayi. Mazauna yankin suka ce an shafe tsawon lokaci ana jin amon manyan bindigogi bayan da maharan suka isa wajen. Ya zuwa yanzu ba a tantance ko su waye suka kai wannan hari ba. A 'yan kwanakin nan kasar ta Mali ta fuskanci kalubale na tsaro batun da ya ke cigaba da haifar da fargabar tabarbarewa lamura na tsaro a wannan kasa wadda 'yan ta'adda suka rika afkawa a 'yan shekarun nan.