′Yan bindiga sun kashe sojojin Mali biyu | Labarai | DW | 27.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan bindiga sun kashe sojojin Mali biyu

Wasu mutane da ake kyautata zaton 'yan jihadi ne a ƙasar Mali, sun kai hari a wannan Asabar ɗin a birnin Nara da ke yammacin ƙasar iyaka da Moritaniya.

Wata majiyar sojan ƙasar ta Mali dai ta bayyana cewar maharan wasu ne daga cikin 'yan ƙungiyar jihadi, kuma 'yan ƙabilar Fulani ne, inda a cewar wata ma'aikaciyar jinya da kuma wani mazaunin birnin na Nara, an ga gawawakin mutane huɗu daga cikin maharan, da kuma sojoji biyu na ƙasar ta Mali. Da misalin ƙarfe bakoye na safe ne dai agogon ƙasar ta Mali aka kai wannan hari, wanda kawo yanzu dakarun sojan ƙasar ke ci gaba da nemansu a lungu-lungu na birnin na Nara.