1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kai hari kan dakarun Mali

Abdul-raheem Hassan
February 24, 2020

Rundunar sojojin kasar Mali ta tabbatar da mutuwar dakarunta hudu tare da jikkatar wasu da dama a wani sabon harin da mayakan jihadi suka kaddamar a sansaninta da ke arewacin kasar.

https://p.dw.com/p/3YGvj
Niger Agadez Wrack eines Selbstmordattentats
Hoto: AFP/B. Hama

Rahotanni na cewa mayakan sun yi awon gaba da motoci da bindigogin sojojin gwamnati bayan bude wuta a sansanin mai tazarar kilomita 100 daga birnin Timbuktu.

Rundunar sojin ta Mali ba ta fadi adadin mayakan da dakarun suka kashe a sabon harin ba, amma shaidu sun ce sun ga 'yan bindigan sun ja gawarwakin kwamandojinsu biyu da sojojin suka kashe. 

Wannan sabon harin dai na zuwa ne bayan da sojojin Faransa suka yi ikirarin halaka mayakan jihadi 50 a  watan Janairun da ya gabata