1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan bindiga sun kashe sojiji 16 a kasar Mali

Binta Aliyu Zurmi
October 1, 2019

Wata kungiya da ke da alaka da Al-Qaida ta kai wani hari a barikin sojojin kasar Mali. Harin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane goma sha shidda ciki harda fararen hula guda biyu. 

https://p.dw.com/p/3Qb1W
Symbolbild Malische Armee (FAMA)
Hoto: Getty Images/AFP/A. Coudurier

Maharan sun isa cikin unguwar da barikin hadayar sojan G5 Sahel da manya-manyan bindigogi a cewar wani kwamandan Sojin kasar Nijar Oumarou Namatou Gazama inda ya dora alhakin harin a kan wata kungiya mai suna Ansarul Islam.

Wani mutum da ke yankin wanda ya nemi a sakaya sunansa  ya tabatar da ganin gawawakin sojoji goma sha biyu  akwance a kasa.

Wannan harin da aka kai a barikin sojin ya yi sanadiyar bacewar manyan bindigogi da ma wasu kayaykin yaki mallakar sojojin a cewar mai magana da yawun gwamnatin kasar ta Mali Yaya Sangare.