′Yan bindiga sun kashe mutane uku a Mali. | Labarai | DW | 05.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan bindiga sun kashe mutane uku a Mali.

Kisan mutanan ya zo a daidai lokacin da a share daya ake zaman sansantawa tsakanin gwamanti da 'yan tawayen kasar Malin a birnin Alger.

A kasar Mali fararan hula uku sun hallaka a sakamakon jerin wasu hare-hare da wasu yan bindiga suka kai a yankin arewacin kasar. Hakan ta wakana ne a daidai lokacin da a share daya gwamnatin da kungiyoyin 'yan tawayen kasar ke zaman tebirin neman sasantawa a birnin Alger na kasar Aljeriya.

A Juma'ar yau dai ake sa ran kawancan kungiyoyin 'yan tawayen abzinawan masu rajin ballewar yankin Azawad daga kasar ta Mali na CMA zai sanya hannu akan yarjejeniyar zaman lafiya domin kawo karshen fadan da ya sake barkewa yau sama da wata daya a yankin arewacin kasar.

A shekara ta 2012 ne dai yankin arewacin kasar mai fama da matsalolin tawaye ya fada a hannun kungiyoyin 'yan ta'adda.Saidai bayan da sojojin kawancan wasu kasashen duniya suka fatattakesu a shekara ta 2013 yankin ya kasa komawa a karkashin milkin Bamako a sakamakon turjiyar kungiyoyin 'yan tawayen Abzinawan yankin.